Fashewar Tukunyar Gas Ya Yi Ajalin Wani Mutum A Kano

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da fashewar tukunyar iskar gas wadda ta yi sanadin mutuwar wani mutum tare da raunata wani, a kauyen Ijarawa da ke Karamar Hukumar Bichi a Jihar.

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Jihar, Alhaji Samisu Abdullahi, ya fitar a ranar Litinin a Kano.

A cewar sanarwar, “Mun samu kiran agaji daka wani jami’in dan sanda mai suna Daiyabu Tukur da misalin karfe 7:46 na safe, cewar wata mota dauke da tukunyar gas ta fadi a kan titi kuma ta yi bindiga.

“Bayan samun kiran, nan take muka aike da jami’anmu wurin da lamarin ya faru da misalin karfe 8:00 na safe don ceto wanda abun ya rutsa da su.

“Wata mota kirar J5 mai lamba FB 52 LAD makare da tukunyar gas a hanyarta ta zuwa Katsina daga Kano ce ta haddasa lamarin,” inji kakakin hukumar.

Abdullahi ya ce lamarin ya rutsa da mutum biyu, Maikano Muhammad mai shekara 45, sai Abdullahi Usman mai shekara 40 wanda ya rasa ransa a sanadin fashewar tukunyar iskar gas din.

“Dukkan wadanda abun ya rutsa da su an mika su ga Usman Usman da ke caji ofis din ‘yan sanda na Bichi. Sannan ana ci gaba da binciken abin da ya haddasa hatsarin,” a cewarsa.

Sanarwar ta kuma ja hankalin direbobi masu daukar abubuwa masu fashewa da su rika kula sosai yayin tuki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button