Cikin ’Yan Kaduna Ya Duri Ruwa Bayan Tashin Abin Fashewa

Hantar mazauna garin Kaduna ta kada inda suka yi ta gudun famfalaki bayan wani abin fashewa da kawo yanzu ba a gano ko mene ne ba ya yi bindiga a wani tsohon otal.

Kakarkin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna, ASP Jalige Mohammed ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an tura jami’an sashen kwance bom na rundunar zuwa wurin da abin ya faru.

Wani jami’in tsaro na JTF ya shaida wa wakilinmu cewa, “Karar da muka ji yana da karfi kuma ya sa cikimu ya duri ruwa, saboda otal din ya dade ba ya aiki. Abun fashewar ya tashi ne a cikin harabar otal din.”

Amma Jalige ya ce ba a samu asarar rai ko rauni ba saboda babu kowa a cikin harabar tsohon otal din.Zuwa lokacin kammala wannan rahoto dai babu wani bayani game da abin da ya haddasa tashin abin fashewar da ya auku da misalin karfe 9.30 na dare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button