Cikin Kuka Ladin Cima Ta Bayyana Cewa BBC Hausa Ba Su Kyata Mata Ba, Domin Sun Yayyanke Maganganun

Cikin Kuka Ladin Cima Ta Bayyana Cewa BBC Hausa Ba Su Kyata Mata Ba, Domin Sun Yayyanke Maganganun Yabo Da Ta Yi Kan ‘Yan Fim
Na yi tsawon minti 45 ina waya da Mama Tambaya bayan ganin hirar ta da BBC Hausa.
Da fari zanso mutane su san cewa duk abunda zan fada a yanzu daga bakin ta ne ya fito, Wannan hira da akayi da Mama Tambaya yau ya kai shekara daya kenan cif.
Mama Tambaya ta ce an yi hiran da ita ne a lokacin da take Quarters kamun ta dawo unguwan da take a nan Mai Dile, ta kuma shaida min cewa a lokacin da ta bar Quarters Ali Nuhu da Kamilu Koko su suka karbe ta hannu bibbiyu suka kuma yi mata goma ta arziki wanda hakan ya zama silar samun muhallin da take ciki a yanzu.
Ta kuma shaida min cewa BBC Hausa basu kyauta mata ba saboda sun cire abubuwa da dama wanda yabo ne da kuma jinjina akan alkairan da yan kannywood suka yi mata kuma suke kan yi!
Wallahi a lokacin da muke wannan magana kuka take yi tana mai cewa inda tasan haka BBC Hausa za su yi mata da ba ta yi hiran nan ba, Saboda sun jawo mata abunda zai 6ata mata suna a gurin yan uwanta kuma abokan sana’anta.
Daraktoci da dama sun sha biyan Mama Tambaya kudi amma sai dai kudin baya isa gare ta wannan shine gaskiya, Kuma ta shaida min cewa ita girmamawa da kyaututtuka da take samu a gurin abokan sana’an ta ya isa ya hana ta zagin kowa ko kuma aibunta kowa don ta gayra kanta.
Daga Sharuzaman Muhammad