Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Hanifa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa tare da yin Allah wadai da kisan dalibar nan mai shekara biyar mai suna Hanifa da aka yi a Jihar Kano.

Shugaban, a cikin wata sanarwar da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar ranar Juma’a, ya kuma jinjina wa jami’an tsaro kan namijin kokarin da suka yi wanda ya kai ga cafke wanda ake zargi da hannu a kisan nata.

A ranar Alhamis ne jami’an tsaro a Jihar Kano suka tabbatar da kisan yarinyar, wacce aka sace tun farkon watan Disamba, kuma ake zargin wani malamin makarantarta mai suna Abdulmalik Tanko da yi, sannan ya binne ta.

Sai dai daga bisani jami’an tsaro sun cafke shi, inda ya ce da shinkafar bera ya yi amfani wajen kisan nata.

Shugaba Buhari ya ce, “Idan abubuwa irin wadannan suka faru, mutane kan yi tsokaci iri-iri kan jami’an tsaro.”

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya jikanta tare da addu’ar Allah Ya ba iyayenta hakurin jure rashinta.

Shugaban ya kuma yi kira ga ’yan sanda da Ma’aikatar Shari’a da su gudanar da zuzzurfan binciken da zai samar da kwararan hujjojin da za su kai ga yin hukunci a kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button