Buhari Ya Yi Alkawarin Kammala Ginin Kasuwar Gold A Kano Kafin Karshen 2022

Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewar za ta kammala ginin kasuwar gwala-gwalai ta jihar Kano kafin karshen shekarar 2022.

shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa kasuwar gwala-gwalan za ta yi gogayya da sauran kasuwannin gwala-gwalai na duniya idan aka kammala ta kafin karshen shekarar 2022.

Wannan batun ya fito ne daga mai ba shugaban kasa shawara a kafofin sadarwa ta zamani, Bashir Ahmed ya fitar a shafinsa na zumunta Twitter, ya ce ministan ma’adinai da karafe,  Olamilekan Adegbite ne ya bayyana wannan babban ci gaban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button