Buhari Bai Taba Ba Da Umarnin Janye Tallafin Mai Ba — Lawan

Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ahmed Lawan, ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai taba ba wa kowa umarnin janye tallafin man fetur ba.

Ya bayyana haka ne a ranar Talata jim kadan bayan gana wa da Buharin a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Lawan ya ce ya gana da Shugaban, ne don tattauna wasu batutuwa da suka shafi mazabarsa, ciki har da janye tallafin man fetur.

Sai dai a watan Oktoban 2021, Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-Tsare, Zainab Ahmed ta sanar da cire tallafin man fetur din da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Ta ce “A kasafin 2022, mun samar da tallafin man fetur iya na rabin shekarar ne, za mu yi kokarin cika ragowar rabin tallafin,” a cewarta.

Sai dai yayin tattaunawar da manema labarai, Shugaban Majalisar ya ce yana da kyau a yi wa jama’a bayani kan lamarin, duba da yadda ’yan majalisar suka shiga damuwa kan yadda ake kokarin tsunduma zanga-zanga a fadin kasar nan.

Ya bayyana jin dadinsa wajen bayyana wa ’yan Najeriya cewar Shugaba Buhari ba shi da hannu wajen ba da umarnin janye tallafin man fetur din.

Ya ce “Yana da kyau ’yan Najeriya su ji abin da muka tattauna da Shugaban Kasa.

“Da yawanmu mun damu da yadda al’ummar kasar nan ke kokawa kan yadda cire tallafin man fetur din ya ta da kura, dole mu kare abin da mutanenmu suke so.

“Mun ziyarci yankunanmu mun tarar da halin da suke ciki, wanda shi ne dalilin da yasa mu ka ga ya kamata mu gana da Shugaban Kasa, a matsayinsa na uban kasa don tattaunawa.

“Mun tattauna kuma abin farin ciki da zan shaida wa ’yan Najeriya shi ne Shugaban bai taba ba wa wani umarnin janye tallafin man fetur ba,” inji Ahmed Lawan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button