Breaking News: JAMB ta kara lokacin yin registration na UTME/DE 2022

Breaking News: JAMB ta kara lokacin yin registration na UTME/DE 2022

Hukumar shirya jarrabawar Jamb ta sanar da kara lokacin registration na wannan shekara kamar yadda ta sanar a jawabinta na sati sati

Hukumar ta sanar da cewar maimakon lokacin da ta fitar 12th Febuary 2022, a yanzu a za’a fara rijistar ne a ranar Asabar, 19th febuary 2022 zuwa ranar Asabar 26th March 2022.

Hukumar tace Karin sati dayanne ( one week) domin ta samarwa dalibai ingatacciyar hanyar yin rijista  wadda kowane dalibi zaiyi alfahari da ita. Dukkan shirye shiryen zasu kammala ne a tsawon wannan sati guda da hukumar ta kara ta inda hukumar zata samu damar karbar dukkan korafe korafen da hukumar ke karba daga dalibai dama ma’aikatanta.

Hukumar na kira da daukacin ai”umma dasu kara hakuri da wannan kari da hukumar tayi a inda tace zata sanar da kammala dukkan shirye shiryenta a website dinta da sauran kafafun yada labarai a ranar Litini 14th Febuary, 2022.

Don haka ke kara kira ga sauran dalibai dasu zauna cikin shiri sukuma tabbatar da bin dukkan ka’idoji da sharuda na hukumar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button