Ban Ji Dadin Sanya Hotona A Labarin Rikicin Kannywood Ba – Rahama Sadau

Ban Ji Daɗin Sanya Hotona A Labarin Rikicin Kannywood Ba, Cewar Rahama Sadau

Fitacciyar jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood, Rahama Sadau, ta koka kan yadda aka sanya hotonta a labarin da aka wallafa kan yadda batun biyan ‘yan fim ya raba kan masana’antar.

Jarumar dai ta ce ba ta ji dadin yadda labarin da sashen Hausa ya wallafa a kan batun ya kunshi hotonta ba a labarin, wanda ya samo asali tun bayan hirar da shashen ya yi da Ladin Chima, daya daga cikin jaruman na Kannywood .

Jarumar ta bayyana hakan a ne a kafar sadarwa ta Twitter inda ta bayyana cewa ita ba tace komai ba a cikin wannan rikici amma kuma BBChausa sun sanya hotonta a cikin jerin wadanda rikicin ya shafa.

Jarumar dai ta sake wallafa labarin a Twitter tare da rubuta”To ni kuma mai ya kawo hotona ciki?, ko neman magana?” a jikin labarin.

Wannan ya sa mutane dake bibiyar shafin tofa albarkacin bakinsu a kai, inda wasu ke ganin kafar BBC ta yi amfani da hoton nata ne domin jan hankalin masu karatu.

Sai dai kuma a cikin labarin, BBC ta bayyana yadda jarumar da ma wasu daban irin su Adam Zango suka nuna nuna alamar yin shiru, duk da sun nuna akwai magana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button