‘Bama-Baman’ Da ’Yan Ta’adda Suka Dasa Sun Fashe A Kauyen Neja

Wasu abubuwan fashewa da ake kyautata zaton bama-bamai ne da ’yan ta’adda suka dasa sun fashe da safiyar Litinin yankin Galadima-Kogo da ke Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Lamarin na zuwa ne ’yan sa’o’i kadan bayan wasu ’yan bindigar sun mamaye kauyuka uku a yankin, ’yan mitoci kadan kusa da garin na Galadima-Kogo.

Har yanzu dai babu cikakkun bayanai a kan yawan mutanen da lamarin ya rutsa da su.

Sai dai wani Shugaban Kungiyar Masu Kishin Shiroro, Sani Abubakar Yusuf Kokki, ya tabbatar wa wakilinmu cewa ana fargabar mutane da dama ne suka rasu.

Muna tafe da karin bayani…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button