Atiku Da Obasanjo Sun Yi Ganawar Sirri

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi wata ganawar siri da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo.

Tattaunawar tasu na zuwa ne kwanaki kadan bayan kotu ta yi watsi da karar da aka shigar na neman ta hana Atiku tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Atiku sun sa labule da Obasanjo ne a safiyar Asabar bayan ya ziyarci tsohon uban gidan nasa a gidansa da ke Abeokuta, Jihar Ogun.

Atiku shi ne wanda ya kasance mataimakin Shugaban Kasa a lokacin mulkin Obasanjo daga shekarar 1999 zuwa 2007.

Sau hudu bayan nan Atiku yana tsayawa takarar zaben shugaban kasa amma ba tare ya kai bantensa ba.

A shekarar 2019 ya tsaya takara a jam’iyyar PDP, amma ya sha kaye a hannun shugaban kasa mai ci, Muhammadu Buhari.

Kawo yanzu dai Atiku bai bayyana matsayarsa game da zaben 2023 da ke matsowa ba, duk da cewa ana rade-radin cewa zai sake fitowa a karo na biyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button