ASUU Da Gwamnati Za Su Koma Teburin Sulhu Ranar Talata

Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU za ta koma teburin sulhu a ranar Talata domin ci gaba da tattaunawa da Gwamnatin Tarayya kan tankiyar da ke tsakaninsu.

A makon da ya gabata ne ASUU ta sanar da tsunduma cikin yajin aikin gargadi na tsawon wata daya saboda rashin cimma bukatun da suka shafe shekara da shekaru suna nema daga gwamnatin tarayya.

Rahotanni sun ce tuni Majalisar Zartarwar Kungiyar suka amince za su tattauna a matsayin share fagen ganawarsu da wakilan gwamnatin tarayya.

Har wa yau, daga cikin manyan muradan da kungiyar ta ke hankoro akwai neman amincewar gwamnatin a kan tsarin biyan albashin ma’aikatan jami’a da ake kira UTAS sabanin wanda gwamnatin ta bijiro da shi na albashin bai daya da ake yi wa lakabi da IPPIS.

Akwai kuma kuma bukatar neman matsaw a gwamnati ta samar da kayyyakin aiki a jami’o’i domin bai wa dalibai damar koyo da kuma gogayya da takwarorinsu na ko ina a duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button