Anyi Sulhu Tsakanin Naziru Sarkin Waka Da Yan Kannywood

Rahotannin yanzu yanzu sun bayyana cewar an yi sulhu a tsakanin jaruman Kannywood da suma yi wata yar gajeriyar sa-in-sa a tsakanin su a makon jiya.

Rahotan yace tsofaffin Jaruman Kannywood ɗin Kabiru Mai Kaba da Ibrahim Mandawari da Shugaban MOPPON Ahmad Sarari, ne suka jagoranci kwamitin sulhun.

Kamar yadda rahotan ya riske mu, tsofaffin jaruman ne suka shiga maganar ganin cewar rigimar tana nema ta wuce gona da iri, a saboda haka ne suka yi gaggawar sulhu a tsakanin jaruman.

An ruwaito cewar an yi sulhun ne a gidan mawakin tsohon sarkin Kano Naziru Ahmad Sarkin waka, dake Jihar Kano da magaribar yau litinin, kuma a dukkan alamu an daidaita.

A lokacin zaman Sulhun akwai Naziru Sarkin waka da Bashir Mai Shadda da Mustapha na Baraska da Musbahu Ahmad da Hadiza Mohammed da jagororin sulhu da kuma sauran masu ruwa da tsaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button