Ansake Gurfanar da makashin yarinyar nan Hanifa

Kotun Majistare ta Kano ta bayar da umarnin mika karar wadanda suka kashe Hanifa zuwa wata babbar kotu, a ci gaba da tsare su a gidan yari.

Wata babbar kotun majistare da ke zamanta a Kano a ranar Laraba ta bayar da umarnin mika Abdulmalik Tanko  zuwa babbar kotu inda ta ce shari’ar ba ta cikin hurumin kotun.

Hausa Drop ta rawaito cewa alkalin kotun majistare dake Kano Muhammad Jibiril ya bayar da umarnin tsare Abdulmalik Tanko da wasu mutane biyu, da ake zargin sun kashe Hanifa Abubakar, yarinya ‘yar shekara 5.

An sake gurfanar da mutane ukun da ake tuhumar su Hashimu Musa da Fatima a gaban Kotun Majistare a ranar Laraba.

Da take zantawa da manema labarai bayan dage zaman darakta mai gabatar da kara na ma’aikatar shari’a ta jihar Kano, Barista Aisha Mahmud ta ce lauyoyin kungiyar sun bayyana ne a madadin gwamnatin jihar.

Ta ce sun nemi kotu da ta mayar da shari’ar zuwa babbar kotun Kano domin ana tuhumar sa da aikata laifuka.

Idan dai ba a manta ba,Hausa Drop ta samu rahoton a ranar 24 ga watan Janairu cewa ‘yan sanda sun gurfanar da Abdulmalik Tanko Hashim Issyaku da Fatima Mus a gaban Alkalin Alkalan Kotun Majistare Mahmud Jibir, a Gidan Murtala, babban birnin Kano, bisa tuhumar su da laifin hada baki, garkuwa da mutane, boyewa da tsare wani da aka sace.

Alkalin kotun, Muhammad Jibrin ya dage sauraron karar zuwa ranar 9 ga watan Fabrairu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button