An Tsige Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta kada kuri’ar tsige Mataimakin Gwamnan Jihar, Mahdi Aliyu Gusau,  ranar Laraba.

‘Yan majalisa 20 daga cikin 24 ne suka kada kuri’ar goyon bayan tsige Mataimakin Gwamnan, bayan kwamitin da majalisar ta kafa da ke bincike a kan zargin shi da almundahana da kudin gwamnatin jihar ya gabatar da rahotonsa.

Related Articles

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasiru Muazu Magarya ne ya karanta rahoton da kwamitin ya gabatar a ranar Laraba, inda ya tabbatar da cewa lallai Mataimakin Gwamnan ya yi sama da fadi da kudin gwamnatin jihar.

Idan ba a manta ba ranar Talata Mataimakin Gwamnan ya ki halartar zaman kwamitin mai mambobi bakwai da ke gudanar da ke bincike a kansa.

Kwamitin binciken

Mai Shari’a Halidu Tanko-Soba ne ya jagoranci Kwamitin, sai Oladipo Okpeseyi (SAN) a matsayin mataimaki.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Abdul Atadoga Ibrahim (SAN) da Hussaini Zakariyau (SAN) da Amina Tanimu Marafa da Alhaji Sani Mande da kuma Ahmad Buhari Rabah.

Bayan gabatar da rahoton binciken, Shugaban Majalisar Dokokin, Nasiru Muazu Magarya ya ce yana da yakinin Kwamitin ya yi bincike a tsanake kuma bisa adalci ga kowane bangare.

“Mun gudanar da aikinmu bisa adalci ga kowane bangare kafin mu tattara hujojji,” inji Shugaban Kwamitin.

Da yake jawabi a kan tsige Mataimakin Gwamnan, Shugaban Majalisar Dokokin ta Jihar Zamfara, Nasiru Muazu Magarya, ya ce za su yi aiki da rahoton a bisa tanade-tanaden sashe na 188 na Kudin Tsarin Mulki.

Ya kuma jinjinawa Kwamitin kan yadda ya gudanar da aikinsa a bisa turbar da Tsarin Mulki ya tanadar.

Shi dai tsigaggen Mataimakin Gwamnan da ne ga tsohon Ministan Tsaro Aliyu Mohammed Gusau, kuma yana cikin mataimakan gwamna mafiya kuruciya a lokacin da ya hau mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button