Abin Da Buhari Zai Yi A Hanyarsa Ta Zuwa Zamfara

Advertisement

Table of Contents

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kama hanyarsa ta zuwa ziyarar aiki Jihar Zamfara.

Shugaban kasar zai fara ne da sauka a Jihar Sakkwato inda zai kafa harsahin gina masana’antar sarrafa siminti na kamfanin BUA, wanda zai samar da metric ton miliyan uku na siminti a shekara; Daga nan kuma ya wuce zuwa Jihar Zamfara.

Tuni dai aka tsaurara matakan tsaro a birnin Sakkwato, gami da taikaita zirga-zirgar ababen hawa a hanyar zuwa masana’antar da Buhari zai kafa harsashin gininsa.

Tun a ranar Talata Shugaban Rukunin Kamfanin BUA, Abdulsalam Isiyaku Rabiu yake ta ganawa da manyan jami’an kamfanin domin ganin komai yana tafiya daidai.

A shekarar 2020 ne Shugaban Kamfanin BUA ya yi alkawarin gina karin masana’antun siminti uku a jihohin Sakkwato da Adamawa da kuma Edo domin kara karfin kamfanin na samar da siminti daga metric ton miliyan 11 zuwa metric ton miliyan 20.

Buhari a Zamfara

Ziyarar Buharin ta ranar Alhamis na zuwa ne bayan sojoji sun tsaurara wajen yi wa ’yan bindiga luguden wuta a jihar, suka kuma karya lagonsu.

Hare-haren sun sa maharan watsuwa zuwa wasu sassa na Jihar Sakkwato, musamman yankin kananan hukumomin Sabon Birni da Isa, inda suka rika yi wa mutane kisan gilla.

Idan ba a manta ba, a kwanakin bayan ’yan bindiga sun tare wata motar fasinja a Sabon Birni inda suka kashe mutum sama da 20 ta hanyar cinna musu wuta a cikin motar.

Kashe-kashen Sakkwato, musamman na Sabon Birni sun haifar da zanga-zanga, saboda a lokacin an zargi Buhari da halartar taron kaddamar da littafin tarihin wani jigo a jam’iyyar APC, Cif Bisi Akande, a Legas, a daidai lokacin da aka yi wa fasinjojin kisan gilla.

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa kaddamar da wasu jiragen yaki da unduanr Sojin Ruwan Najeriya ta kera ne ya kai shi Legas, ba wai musamman domin halartar kaddamar da littafin ba.

Buhari ya kuma tura tawaga ta musamman wadda ta kunshi manyan hafsoshin tsaro domin yin ta’aziyya da kuma daukar matakan kakkabe ayyukan ’yan bindiga.

A kwanakin baya ba hukumomi a Jihar Zamfara sun ce maharan suna neman a yi sulhu da su domin su daina aika ta’addancinsu.

Idan ba a manta ba a kokarin murkushe ’yan bindiga, a baya gwamnati ta rufe layukan sadarwa a Jihar Zamfara da kuma Katsina da Neja da

Source: Aminiya Dailytrust

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button