News

Saurayin diyata da na Aura Mutumin Kirki ne – Khadija Rano

Yadda aka yi na auri saurayin diyarta- Khadija Rano

Wata mata daga jihar Kano da aka bayyana sunanta da Malama Khadija yar asalin karamar hukumar Rano ta kashe aurenta sannan ta auri saurayin diyarta.

 

Majiyar DCL Hausa ta jaridar Daily trust ta ruwaito cewa ‘yan uwan ​​Khadijah sun zargi kwamandan Hisbah na karamar hukumar Rano da bayar da auren ‘yarsu ba tare da yardar su ba, asali ma ba su ma san inda take ba.

Sai dai da take magana da gidan rediyon, Freedom Radio, Malama Khadija ta bayyana cewa tana cikin koshin lafiya kuma tana rayuwarta cikin jin dadi da sabon mijin nata.

Khadija ta ce a lokacin da diyarta Aisha ta yanke shawarar ba za ta auri mutumin ba, sai ta ji bai kamata su biyu su rasa shi ba domin ita ya riga ya kwanta mata a rai don haka ta yanke shawarar tuntubar danginsa don neman izinin aure shi.

Ta ce, “Ban yi hakan ba bisa jahilci sai da na tuntubi malamai suka ce ba a haramta ba. Kuna na tuntube shi, ya amince, amma iyayena da ’yan uwana sun ki na aure shi. Hakan ne ya sa na yanke shawarar garzayawa hukumar Hisbah suka daura mana aure, kuma yanzu haka muna cikin farin ciki ni da mijina.”

Sai dai Kawun Malama Khadija, Abdullahi Musa Rano, ya bayyana abin da ta yi a matsayin abin kunya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button