News

Abin da ya sa amfani da internet ke samun cikas a Indiya

To sai dai ƙaruwar amfani da internet a ƙasar na ci gaba da samun cikas.

 

Indiya ta kasance ƙasa ta biyu a duniya a fannin kasuwar waya, inda take da sama da mutum biliyan guda masu amfani da waya.

A watan Oktoban 2021, hukumar da ke lura da fasahar sadarwar ƙasar ta ce akwai masu amfani da internet kimanin miliyan 790 a wayoyin hannunsu.

Kimanin ƙarin mutum miliyan guda na masu amfani da internet a watan Agustan 2021.

To sai dai a yanzu masu amfani da internet a wayoyinsu na ci gaba da raguwa.

Manyan wayoyin hannu, su ne manyan hanyoyin amfani da internet, kuma su ne raguwar ta fi shafa.

Indiya na da masu amfani da manyan wayoyi miliyan 650, to sai a yanzu yawan mutanen na ci gaba da raguwa.

Shagunan sayar da wayoyi sun ragu daga shago miliyan 160 a shekarar 2021 zuwa miliyan 151 a yanzu, kamar yadda cibiyar Counterpoint da ke binciken a fannin kasuwanci a ƙasar ta bayyana.

Ana kuma hasashen raguwar za ta ƙaru matuƙa a wannan shekara.

Shekara uku da suka wuce, masu amfani da manyan wayoyi kan sauya wayoyinsu cikin watannin 14 zuwa 16, kamar yadda cibiyar lura da harkokin cinikayya ta IDC ta bayyana. To amma a yanzu mutane kan sauya wayoyin nasu cikin watanni 22 ko fiye.

Dalili kuwa shi ne farashin wayoyin ya yi tashin gwauron zaɓo tun bayan ɓarkewar annobar korona, da karyewar farashin kuɗin ƙasar da kuma samun tsaiko wajen shiga da wasu kayyakin ƙera wayoyin daga ƙasar China, wadda ita ce ƙasa ta farko a duniya a harkokin kasuwancin wayoyin hannu.

Kusan kashi 90 na abubuwan da ake buƙata domin ƙera wayoyin hannu a Indiya ana shigar da su ƙasar ne daga ƙasashen waje.

Matsakaicin farashin babbar waya a Indiya yanzu ya kai rupee 22,000 kimanin dala 269, saɓanin rupee 15,000 da ake sayar da ita shekara biyu da suka gabata, kamar yadda wani jami’i a cibiyar IDC ya bayyana.

“Wanna shi ne dalilin da ya haddasa raguwar amfani da internet. Ƙasar da ke matsayi na biyu, a fannin cinikayyar wayoyin hannu a duniya, na fuskantar cikas a fannin internet” in ji jami’in na IDC.

Indiya na da masu amfani da ƙananan wayoyin hannu sama da miliyan 350, waɗanda kuma ka iya komawa amfani da manyan wayoyin hannu idan suka samu dama. Kusan rabin waɗannan mutane na amfani da wayoyin da farashinsu bai kai rupee 1,500 ba.

Sakamakon tashin farashin wayoyin da kuma data, mutum miliyan 35 ne kawai suka samu damar komawa amfani da manyan wayoyi a shekarar 2022, saɓanin miliyan 60 da ake samu a kowacce shekara a baya, kamar yadda cibiyar Tarun Pathak of Counterpoint mai binciken kasuwanci ta bayyana.

Raguwar amfani da internet mummunan labari ne ga Indiya. Domin kuwa zai yi wa ‘yan ƙasar matuƙar wahala su iya amfana da tsare-tsaren gwamnati, kamar bayar da tallafi da allurar riga-kafi da sauransu.

Adadin masu amfani da internet a yankunan karkara na ci gaba da raguwa.

Haka kuma bayanai daga cibiyar lura da masu amfani da internet ta ƙasar (AIMAI) sun nuna cewa maza sun fi mata samun damar amfani da manyan wayoyi.

Kuma a yankunan karkara wasu iyalan kan yi amfani da waya ɗaya a gida guda.

To sai dai Mista Pahwa na cibiyar AIMAI ya ce ba ƙaruwar farashin wayoyi ba ne ya haddasa raguwar amfani a internet a ƙasar ba.

A ganinsa ya kamata masu ƙirkirar manhajojin da ake amfani da su a manyan wayoyi da su riƙa lura da bambancin harshe da kuma yanayin ilimi musamman ga mazauna karkara. Mafi yawan manhajojin na amfani da harshen Ingilishi da kuma wasu ƙalilan na harsunan ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button