Na Damu Matuka Da Yadda Sanatoci Ke Ficewa Daga APC – Abdullahi Adamu

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya nuna damuwarsa kan yadda Sanatoci ke ci gaba da ficewa daga jam’iyyar.

Sanatoci bakwai ne dai suka fice daga APC bayan sun gaza samun tikitin tsayawa takara a cikinta a zaben 2023 mai zuwa.

Wadanda suka fice din sun hada da Ibrahim Shekarau (Kano), Yahaya Abdullahi (Kebbi) Adamu Aliero (Kebbi), Dauda Jika (Bauchi), Ahmad Babba Kaita (Katsina), Lawal Yahaya Gumau (Bauchi) da kuma Francis Alimikhena (Edo).

Da yake zantawa da manema labarai bayan wani taron sirri da Sanatocin APC a Abuja, Shugaban jam’iyyar ya ce abin takaice ne yadda ake ficewa daga cikinta.

Ya ce, “A kowacce shekarar zabe, irin wadannan abubuwan ba sababbi ba ne. Najeriya da APC kuma ba za su zama na daban ba.

“Saboda haka, ni ban damu da me ke faruwa a wasu jam’iyyun ba, APC ce a gabana.

“Ba a iya APC hakan ke faruwa ba, amma da yake mu ne jam’iyya mai mulki, shi ya sa matsalarmu ta fi fitowa fili.

“Babu shugaban da ya san abin da yake yi da ba zai damu ba idan ya yi asarar ko da mutum daya, ballantana biyu ko uku,” inji Abdullahi Adamu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button