APC ta nada Ganduje shugaban yakin neman zaben Gwamnan jihar Osun

Abuja – Uwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ta sanar da mambobin kwamiti mutum 81 da zasu yiwa jam’iyyar yakin neman zaben gwamnan jihar Osun.

Hukumar INEC zata gudanar da zaben gwamnan jihar ne ranar 16 ga Yuli, 2022.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Gwamnan Legas Babajide Sanwoolu, aka nada su jagoranci kwamitin.

A jerin sunayen da shugaban uwar jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu, ya fitar ranar Talata, yace an baiwa wannan kwamiti hakkin tabbatar da cewa dan takarar jam’iyyar, Gboyega Oyetola, ya lashe zaben.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila. Za’a rantsar da kwamitin ranar Alhamis a sakatariyar jam’iyyar dake Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button