Sheikh Dr. Ahmad Gumi yayi kakkausar jan kunne ga wadanda suka kashe Deborah, ya ce ba hurumin su bane yanke hukuncin kisa don an zagi Annabi SAW

A yayin da wasu malaman ke nuna jin dadin su ga abinda Samarin jihar Sokoto suka aikata akan matashiyar nan da tai batanci ga fiyayan Halitta Annabi Muhammad (SAW) Shikuma Sheikh Ahmad Gumi Nuna rashin jin dadin sa ga abinda Matasan sukai inda yay kakausan kalamai ga wannan matasa kaman haka:

Idan Deborah ta Zagi Annabi, kamata yayi a kai karanta wajen hukumar makarantar, daganan kuma sukai ga sultan sannan gwamnati ta shiga ciki, amma ba kawai ku suntumi makamai ba ku kashe ta.

Kaman yadda kuka sani Deborah itace dalibar Kwalegin Shehu Shagari dake Sokoto wadda tai batanci ga fiyayen halita Annabi Muhammad wadda dunbin matasa suka halaka ta nan take.

Sanadiyar da yasa jami’an tsaron suka kama muttun biyu dake da hannu a kisan hakan, wanda hakan ya jawo tarin matasan jihar da daliban makarantar suka fito zanga zanga akan a saki wannan dalibai guda biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button