Mun Bar Wa Allah Komai, Shi Zai Daukar Mana Mataki Kan Kashe ‘Yarmu Da Aka Yi, Cewar Iyayen Deborah Yakubu

Iyayen dalibar da aka kashe a Sokoto kan zargin batanci kan Annabi Muhammad SAW, sun bayyana cewa sun mika komai ga Allah, shi daukar musu mataki.

Emmanuel Garba da Alheri Emmanuel a lokacin da suke zantawa da manema labarai sun ce, “Ba za mu iya cewa ko yin komai ba, sai dai mun bawar Allah komi shi zau kan mana mataki akan abunda aka yi mana.

A jiyane dai wasu hotuna sukaita yawo a kafofin sada zumunta inda akaga gawar Deborah an dauketa awata mota izuw kabarinta, haka zalika awajan binne gawar tata mutanen dasukaje basu wuce mutum 10 ba.

Ayanzu dai haka sakamakon zanga zangar da mutane suka fito ranar asabar sukayi wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutum daya tareda jikkata mutum biyu, wannan dalilin yasa gwamnatin jahar sokoto ta sanya dokar kulle ta tsawon awanni ashirin da hudu, domin samun daidaito da zaman lafiya a jahar.

Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna HausaDrop.Com domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button