2023: Zan Goyi Bayan Duk Dan Takarar Da PDP Ta Tsayar – Bala Mohammed

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce a shirye yake ya mara baya ga duk wanda ya lashe zaben fid da gwanin takarar Shugaban Kasa a jam’iyyarsu ta PDP.

Bala ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala rangadin neman goyon bayan daliget a jihohin Anambra da Ebonyi da kuma Enugu.

Ya bayyana hakan ne duk da yana ci gaba da takarar a jam’iyyar.

Yayin rangadin nasa, Gwamna Bala ya bukaci daliget din jihohin da ya ziyarta kan su zabe shi yayin zaben fid da gwanin da PDP za ta gudanar a tsakanin ranakun 28 da 29 na watan Mayu.

Gwamnan ya ce yana da kwarewa da kuma cancantar da ake bukata wajen bunkasa kasa da al’ummarta yadda ya kamata.

Ya ce, “Ina mai gabatar muku da kaina don ku zabe ni, don haka nake neman goyon bayanku, amma idan ya zamana ban yi nasara ba a zaben, zan mara wa duk dan takarar da PDP ta tsayar a karshe don mu ceci Najeriya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button