Shekarau Ya Dage Taron Da Ya Shirya Yau Asabar Kan Matsayarsa A Rikicinsa Da Tsagin Ganduje

Tunda farko dai tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, a makon da ya gabata ya bayyana cewa a yau Asabar 14, ga watan mayun 2022, zai bayyana matsayarsa ta karshe a siyasance dangane da rikicinsa da tsagin gwamna Ganduje cikin Jam’Iyyar APC.

Sanarwar dage taron wadda aka wallafa ta a shafin facebook na hadimin Sanatan a kafafen sadarwar zamani, Ismail Lamido, ta ce an dage taron da aka shirya a yau Asabar.

“An dage taron da aka shirya yi yau asabar a gidan, Mal Ibrahim Shekarau, za a sanar da ranar da taron zai kasance insha Allah nan gaba kadan,”

“Dage wannan taro ba shi da nasaba da sulhun da jam’iyyar APC take so a yi a kurarren lokaci,” In ji Lamido

Sanarwar ta yi karin haske dangane da dalilan dage taron kamar haka, “Akwai muhimman abubuwa da ake karasa shirya wa tsakanin manyan jagororin da zasu hadu don ceto Kano, wato Madugu Uban tafiya da Malam Mai ta Annabi.” Cewar Ismail Lamido

Sai dai wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta, ta bayyana cewa dage taron yana da alaka da irin kyakkyawan shirin da ake son yi na karbar Sanata Shekarau din a Jam’iyyar NNPP da sauran batutuwa masu nasaba da kulla yarjejeniyar siyasa gabanin kafa sabuwar gwamnatin Kano tsakanin Jagororin biyu.

Tun da farko dai a daren jiya Gwamna Ganduje ya ziyarci gidan Malam Shekarau a Mundubawa don lallashinsa da ya bi shi su tafi Abuja don yin sulhu.

Source: Leadership Hausa


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button