An birne Deborah, dalibar da aka kashe kan batanci ga Manzon Allah (SAW)

An birne Deborah Samuel, dalibar kwalejin ilmin Shehu Shagari da aka kashe a jihar Sokoto kan laifin kalaman batancin ga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata gareshi).

TheNation ta ruwaito cewa an birne Deborah ne a mahaifarta, Tunga Magajiya, dake karamar hukumar Rijau a jihar Neja.

An birneta misalin karfe 6:30 na yamma a makabartar Kirista dake Tunga Magajiya.

Da farko matasan garin Tunga Magajiya sun ki amincewa a birneta inda suka ce gwamnatin jihar Sokoto ya kamata su dau nauyin jana’izar.

Amma babba yayanta wanda Fasto na a cocin ECWA< Emmanuel Maaji, ya jagoranci bizneta.

Source: Legit.ng


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button