Gombe: Mai adaidaita sahu ya yi garkuwa da kansa don ya samu N500,000 ya biya bashin da ‘yar uwarsa ke binsa

Gombe – Jami’an yan sanda a jihar Gombe sun kama wani Halilu Aliyu, mai adaidaita sahu, saboda yin karyar cewa an yi garkuwa da shi saboda bashin N250,000 da ake binsa, The Punch ta ruwaito.

Ita ma The Cable ta ruwaito cewa an kama Aliyu, mai shekaru 32, tare da Ahmed Ladan, mai shekaru 42, wanda ake zargi tare suka kitsa makircin.

Yan sandan sun ce wanda ake zargin ya fada matsala ne bayan ya sayar da keke napep din da yar uwarsa ta bashi domin ya yi kasuwanci.

An ce Aliyu ya bullo da wannan shirin ne domin ya samu kudin da zai biya ‘yar uwarsa kudinta duba da cewa tana tambayan inda keke napep dinta ya ke.

Mary Malum, mai magana da yawun yan sandan Gombe ta ce:

“Yar uwarsa ne ta bawa wanda ake zargin na farko, Haliru Aliyu, namiji, mazaunin Tudun Wada quarters a Gombe adaidaita sahu bayan kasuwancinsa ya rushe.”

“Amma daga bisani, wanda ake zargin ya sayar da adaidaita sahun ba tare da sanin mai shi ba a kan N250,000.

“Da mai keken ta tambaya keken ta ko kudi, wanda ake zargin ya gaza biya.

“Saboda kunya a cewarsa, a ranar 30 ga watan Disambar 2021, wanda ake zargin ya tafi gidan abokinsa, wanda ake zargi na biyu, wani Ahmed Ladan, inda suka kitsa garkuwa na karya domin su amshi kudi hannun yayansa Zainab Aliyu, kudi N500,000 don ya samu ya biya bashin.”


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button