Matashiya Ta Kashe Kanta Bayan An Yada Hotunan Tsiraicinta A Masar

Wata matashiya mai shekara 17 ta kashe kanta bayan sakin hotunan tsiraicinta da wasu matasa biyu suka yi a kasar Masar.

Bayan mutuwar matashiyar mai suna Busant Khalid, jami’an tsaro sun cafke matasan biyu da ake zargin sun yada hotunan tsiraicin nata.

’Yar uwar matashiyar ta shaida wa manema labarai cewa an hada hotunan karya na ’yar uwarta sannan aka yada a kafafen sada zumunta, wanda hakan ya jefa ta cikin damuwa.

Wasu daga cikin abokan matashiyar sun bayyana cewa kafin mutuwarta ta shiga damuwa wanda babu wanda yake da masaniyar abin da ke damun ta.

Sai dai labarin kashe kanta da ta yi ya jawo ce-ce-kuce a tsakanin ma’abota amfani da kafafen sada zumunta a kasar.

Tuni dai aka kirkiri take da “Basant_Khaled’s_right_must_be_returned” a Twitter, inda ake neman bin ba’asi tare da kwato mata hakkinta.

Mutane da dama sun wallafa hotunan matashiyar a kafafen sada zumuntarsu don nuna goyon baya tare da nema mata adalci.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button