Ƴan bindiga sun sace ƴan China a jihar Neja

Wasu ƴan bindiga sun sace wasu ƴan China huɗu tare da kashe masu tsaron su biyu a jihar Neja da ke yankin tsakiyar Najeriya.

Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Ahmad Matani ne ya tabbatar wa da BBC lamarin wanda ya faru a jiya Talata.

Ƴan bindigar sun sace ƴan Chinar ne da ke aiki a Madatsar Ruwa ta Zungeru.

Source: Bbc Hausa


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button