‘Yan biyun da aka haifa a shekara daban-daban a 2021 da 2022

An haifi wasu ƴan biyu a shekara daban-daban a Amurka, a shekarar 2021 da kuma 2022.

Minti 15 ne tsakanin haihuwar tagwayen wanda ya raba shekarunsu.

An haifi tawagyen ne a wata asibiti da ke Salinas, jihar California.

An fara haihuwar namiji a 2021, bayan minti 15, kuma bayan shiga sabuwar shekara aka haifi mace a 2022.

Asibitin Navidad da aka haifi jaririnan ne ya sanar da al’amarin a Twitter wanda ba a saba gani ba.

Hakan na nufin an samu banbamcin rana da wata da kuma shekara a takardar shedar haihuwarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button