Tirƙashi An yi awon gaba da wata amarya mai suna Farmat Paul sa’o’i kafin bikinta a Jihar Filato.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi awon gaba da wata amarya mai suna Farmat Paul sa’o’i kafin bikinta a Jihar Filato.

Wani mazaunin yankin Ngyong a Karamar Hukumar Bokkos ta Jihar Filato ya ce an sace amaryar ce a gidan limamin da zai daura mata aure wanda a nan ake sa ran za ta kwana kafin bikin.

Ganau sun ce yan bindiga kai tsaye suka afka gidan limamin da misalin karfe 10.45 na dare inda suka yi awon gaba da amaryar ita kadai.

Ganau sun ce yan bindiga kai tsaye suka afka gidan limamin da misalin karfe 10.45 na dare inda suka yi awon gaba da amaryar ita kadai.

Majiyoyi daga wasu makusantanta sun shaida wa wakilinmu cewa an shirya gudanar da daurin auren a ranar Lahadi a yankin na Ngyong.

Yayin da wakilinmu ya tuntubi jami’in hulda da al’umma na rundunar ƴan sandan jihar ASP Ubah Gabriel Ogiba ya ce ba a kai musu rahoton faruwar lamarin ba, amma dai sun samu labari kuma tuni suka shiga gudanar da bincike da bibiyar sahunta.

Sai dai ASP Ogiba ya ce ta yiwu ba sace amaryar aka yi ba domin kuwa a cewarsa irin haka ta faru da wata mace da ta tafi wani gidan domin ta kwana amma aka rika yayata cewa sace ta aka yi.

To jama’a zamuso mukarɓi ra’ayoyin akan aukuwar wannan lamari don jin tabakinku zamuso kubiyomu kaitsaye tasahinmu na tsokaci kaitsaye.

Source: DalaTopNews


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button