Yanzu Yanzu: Nafisa Abdullahi ta fita daga Shirin Labarina

Tauraruwar fina-finan Kannywood, Nafisa Abdullahi, ta ce daga yanzu ba za ta ci gaba da fitowa a shirin nan mai dogon zango mai suna ‘Labarina’ ba.

A sakon da ta wallafa a shafinta na Intagram ranar Asabar da daddare, tauraruwar ta ce ta ji dadin rawar da ta taka a cikin shirin, sai dai ta ce ba za ta iya ci gaba da shi ba saboda wasu dalilai na kashin kanta.

Amma wasu majiyoyi sun tabbatar wa BBC Hausa cewa ta dauki matakin ne saboda rashin jituwar da aka samu tsakaninta da mai shirya shirin kuma shugaban kamfanin Saira Movies, Malam Aminu Saira.

Nafisa Abdullahi ita ce babbar tauraruwa a shirin na Labarina mai farin jini a tsakanin ‘yan kallo inda take taka rawa a matsayin Sumayya.

Nafisa Abdullahi ita ce babbar tauraruwa a shirin na Labarina mai farin jini a tsakanin ‘yan kallo inda take taka rawa a matsayin Sumayya

Janyewata daga [shirin] a wannan lokaci ya faru ne saboda yawan da ayyuka da suka yi mini, ganin cewa hakan ba zai ba ni damar shiga wajen daukar fim din na ‘Labarina’ ba,” a cewar tauraruwar.


Follow Hausadrop On Facebook

2 Comments

  1. Ina gaisuwa zuwa ga fitacciyar jaruman nan
    Nafisa Abdullahi, da ta yi hakuri ta koma cikin Shirin labarina Don a gaskiya muna bukatar ta sosai, a halin yanzu duk da yake ban San abinda yasa ba, don Allah

  2. Ina gaisuwa zuwa ga fitacciyar jaruman nan
    Nafisa Abdullahi, da ta yi hakuri ta koma cikin Shirin labarina Don a gaskiya muna bukatar ta sosai, a halin yanzu duk da yake ban San abinda yasa ba, don Allah

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button