Wani kamfani ya maka jaruma Hafsat Idris a kotu dalilin cinye musu kudi da tayi Naira Miliyan 1 da dubu dari 3

Wani kamfani ya maka jaruma Hafsat Idris a kotu dalilin cinye musu kudi da tayi Naira Miliyan 1 da dubu dari 3

Wani rahoto da gidan Radiyon Dala FM dake jihar Kano ya fitar ya bayyana cewa: Wani kamfani yayi karan jarumar masana’antar kannywood Hafsat Idris zuwa babbar kotun jihar Kano wanda ke ungoggo.

Kamfanin yayi karan jaruma Hafsat Idris ne dalilin cinye zunzurutun makudan kudade har Naira Miliyan 1 da dubu dari 3 wanda aka taba domin ta dauki bidiyon rawa, amma jarumar ta saba alkawari taki daukar bidiyon.

Inda rahoton ya bayyana cewa: Jaruma Hafsat Idris taje wajan bikin inda har an fara daukar bidiyon amma sai jarumar ta gudu bata dawo ba, inda hakan yasa kamfanin yake yayi karanta yake bukata kotun tasa jarumar ta dawo musu da wadannan kudaden, sannan kuma ta biya su Naira Miliyan 10.

Kamfanin ya bukaci jaruma Hafsat Idris ta biya wannan kudin Naira Miliyan 10 a maimakon diyyar asarar da suka yi, domin sun gayyaci ma’aikata sannan kuma sun dauko kayan aiki amma rashin cika alkawari da jarumar tayi musu yasa suka yi wannan asara.

Amma har kawo wannan lakocin babu wanda yaji ta bakin jaruma Hafsat Idris, amma zuwa gaba ba’a san mai jarumar zata fito ta fada ba.

Ku kasance damu a wannan shafi namu na Hausadrop.com, domin samin wasu labaran namu a duk sanda muka wallafa, sannan kuma muna bukatar ku danna alamar subscribe domin labaran namu suna isa gareku a duk sanda muka wallafa su mungode.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button