Sadiya haruna ta wallafa wata bidiyo tana nuna rashin jin dadin ta kan abin da Auwal isab west ya yiwa jaruma Hadiza gabon

Sadiya haruna ta wallafa wata bidiyo tana nuna rashin jin dadin ta kan abin da Auwal isab west ya yiwa jaruma Hadiza gabon

Kamar yadda kuka sani a yanzu ne ake tsaka da rigima tsakanin jaruma Hadiza gabon da Auwal isah west wanda rigimar tasu ta janyo cece-kuce da maganganu a kafafan sada zumunta.

Da farko dai jaruma Hadiza gabon tayi martani ne ga wasu jaruman masana’antar kannywood wanda suka halarci wajan shagalin bikin BBNaija domin su taya wani jarumin gidan murna dalilin wata gasa daya lashe.

Daga nan ne kuma sai jarumi Auwal isah west ya wallafa wata bidiyo inda yake zagin jaruma Hadiza gabon har ma da fadin wasu maganganu wanda basu dace ba, inda yayi ta chin zarafinta a cikin wannan bidiyo daya wallafa.

Sai kuma a yanzu muka sami wata bidiyo ta Sadiya haruna wanda ta wallafa a shafinta na instagram tana magana akan wannan abin da Auwal isah west ya yiwa jaruma Hadiza gabon, inda take nuna rashin jin dadin ta kan hakan wanda har ma ake ganin kamar tana bin dayan Hadiza gabion ne sai dai ta fadi cewa ba bayan ta take bi ba gaskiya take fada.

Kalli bidiyon domin kaji abin da Sadiya haruna take fada kan wannan maganganu da Auwal isah west yayiwa Hadiza gabon.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button