Mata biyu 2 a kannywood sun ishemu darasi, cewar Sunusi Oscar 443 mai bada umarni

kamar yadda kuka sani abubuwa da dama suna faruwa a masana’antar kannywood wanda suke zama izna da kuma abin lura ga duk wanda yake cikin masana’antar ta kannywod.

Babban mai bada umarni a cikin masana’antar ta kannywood Sunusi Oscar 442 ya fadi wata magana da tazama abin cece-kuce a shafukan sada zumunta.

a wannan masana’antar ta shirya fina-finan hausa ta kannywood anyi jarumai da dama wanda ake kwatance dasu sannan kuma sun shahara a lokacin da suke kan ganiyarsu, wanda haka yanzu wasu daga cikin su sun bar duniya wasu kuma suna nan a raye amma sunbar harkar ta fim wanda ko duriyar su ba’a ji.

duk wanda ya yasan maicece rayuwa to hakika bazai na nuna girman kai ba ko jiji da kai sabida ita rayuwa juyi-juyi ce, a wasu shekaru da suka shude anyi wasu jarumai masana’antar kannywood wanda wanda suka shahara sannan kuma daukakar su tayi tasiri, a cikin wadannan jaruman akwai irin su jaruma Balaraba muhammad, Ahmad S Nuhu, Hauwa Ali Dodo wanda aka fi sanin ta da Biba problem, wanda dukansu sun bar duniya sun koma ga mahaliccinsu.

Haka kuma a masana’antar kannywood a yanzu a kwai jarumai mata irin su Ummi zezee, Fatima Muhammad, Fati Baffa fage, wanda duk suna raye har yanzu amma sun dai an harkar fim.

Sai dai kuma a wannan zamani da muke ciki a kwai wasu jarumai a masana’antar ta kannywood wanda rayuwar da suke ya kamata ta zama darasi akan wasu, kamar yadda mai bada umarni a masana’amtar wato Sunusi Oscar ya wallafa a shafinsa na sada zumunta instagram.

inda yake fadin cewa mata biyu 2 a kannywood sun ishemu darasi.

Amma sai dai Sunusi Oscar mai bayyana ko suwaye wadannan jaruman ba, amma sai dai wasu daga cikin mabiyan sa sun tofa albarkacin bakin su kan wannan wallafar da yayi kamar yadda zakuga kofarin nasu a kasa.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button