Kalli wasu kyawawan jarumai mata na masana’antar kannywood wanda tauraruwar su take haskakawa a yanzu

Kalli wasu kyawawan jarumai mata na masana'antar kannywood wanda tauraruwar su take haskakawa a yanzu

Masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood ba tun yanzu ba ta saba tara kyawawan jarumai mata wanda sukan dauki hankulan al’umma, wanda tun a shekarun baya masana’antar dama ta saba tara irin wadannan jaruman.

Har kawo yanzu masana’antar kannywood bata dai na sanya kyawawan jarumai mata a shirin fina-finan su ba, domin ta dalilin wadannan matan ake yawa bibiyar wasu fina-finan har ma su sami daukaka daga wajan al’umma masu kallon shirin nasu.

A ‘yan kwanakin nan masana’antar ta kannywood ta sake karo wasu kyawawan matan domin cigaba da shirin fina-finai masu dogon zango, sannan kuma jaruman sun kasance masu matsakaitan shekaru wanda shirin zai yi dai dai da shekarun nasu.

Ayau kuma muka sami wata bidiyo wanda tashar Arewa package ta kan manhajar Youtube ta wallafa wasu kyawawan jarumai 10 na masana’antar ta kannywood wanda tauraruwar su take kan haskakawa.

A cikin bidiyon zakuga yadda tashar ta Arewa package ta jero kyawawan jaruman daya bayan daya, wanda duk wanda ya kalli wadannan jaruman tabbas zai gaskata kyawawa ne

Wadannan jaruman ana sa ran zuwa nan gaba zasu iya mayewa gurbin da wasu jarumai suke jan ragama a yanzu a masana’antar ta kannywood.

Ga bidiyon nan domin ku kalla sukan wadannan kyawawan jaruman wanda tauraruwar su take haskakawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button