Jarumin kannywood Mustapha Nabraska yace babu adawa a tsakaninsa da Ganduje gwamnan Kano

Jarumin kannywood Mustapha Nabraska yace babu adawa a tsakaninsa da Ganduje gwamnan Kano

Ficaccan jarumi a masana’antar kannywood Mustapha Nabraska wanda yake gudanar da harkokin siyasa a karkashin jam’iyyar (P.D.P) ya bayyanawa al’umma cewa baby wata adawa a tsakanin sa da Gwamnatin jihar Kano.

Jarumi Mustapha Nabraska ya fadi haka ne a shirar da sukayi da Freedom Radio inda ya kara da cewa: Sasancin da sukayi da Gwamnatin jihar Kano ba karamin ci gaba suka sami ba cikin dan kankanin lokaci, amma hakan ba wai yana nufin yin siyasa bane sai dai alakar yin aiki tare da kuma mutunta juna kawai.

Sannan jarumi Mustapha Nabraska ya bayyana cewa: Gwamnatin baya ba karamar asara ta janyowa masana’antar harkar fina-finai ta kannywood ba, sabida mafi yawan daraktocin masana’antar wanda suke shirya fim sai da sukabar jihar Kano suka koma wasu jahohin sannan sukaci gaba da ayyukan su.

Jarumin ya kara da cewa: Har kawo yanzu suna samin kalubale amma tunda suka nemo bakin zaren sun fara samin sauki, domin kuwa a yanzu sun daina bin wata doma ko tsari na shugabancin hukumar tace fina-finan hausa ta kannywood.

Inda yake cewa: Kawai dai suna yin abin da sukaga yafi dacewa sabida hakane ma suke yiwa hukumar karan tsaye, domin duk wata matsala da suke samu tana da alaka da shugabancin hukumar tace fina-finan.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button