Jaruma Ummi Rahab ta bayyana abinda ke tsakaninta da Adam A Zango.

Yar wasar kwaikwayo na masana’antar Kannywood wacce akafi sani da Ummi Rahab, ta yi magana kan dambarwar da take tsakaninta da shararren dan wasan Kannywood kuma mawaki wanda yake a matsayin uba gareta ita Ummi Rahab din wanda ita da kanta ta bayyana hakan tace, “Adam A. Zango tamkar uba yake a wajena.

A hirar da tayi da wani gidan jarida Ummi Rahab ta bayyana cewa Adam A Zango ya cire ta daga wasu fina-finai da ya kamata ace ta fito a ciki.

Amma a ra’ayinta, wannan ba komai bane saboda a matsayinsa na ubangidanta, yana da ikon daze cireta daga Film ko kuma ya sakata.

Yayinda aka tambayeta kan lamarin dayasa aka cireta a Film din tace:

“Gaskiya hakane, amma wannan ba komai bane tunda yana da ikon daze cire ko kuma ya saka wanda yaga dama a film dinsa”

Kuma ta qara da cewa “Babu shakka ina daga cikin wadanda aka shirya za su fito a cikin fim dinsa me suna ‘Farin Wata Sha Kallo’ da ake nunawa a YouTube, amma ban san dalilin daya saka ba sai suka cire ni.”

Kishi ke damunsa

A hirar da mukayi da jaruma ummi rahab dani da sauran abokan aikina jaruma Ummi Rahab ta kara da cewa

“Adam A Zango na kishi ne kawai saboda tana soyayya da wani sabaninsa duk da yayi kokarin hanata.”

A cewarta, Adam A Zango na matsayin Uba ne gareta amma da alamun bai fahimci hakan ba.

Sannan kuma tace

“Na fada wa wadansu daga cikin aminaina cewa Adam A Zango yana kishi ne saboda na fara soyayya da wadansu samari wadanda shi baison tarayyata dasu, ya yi kokarin ya hana ni, amma na nuna masa cewa shi fa uba ne gareni.

Da ya ga ba zan yarda da ra’ayinsa ba shi ne ya fara yimin bore wannan kawai shine abinda ke tsakanina dashi.”

BY HAUSADROP. COM

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button