Jaruma Hadiza gabon ta soki Ali buhu sabida shishigin da yayi na zuwa wajan taron shirin Big brother

Jaruma Hadiza gabon ta soki Ali buhu sabida shishigin da yayi na zuwa wajan taron shirin Big brother

Jarumar kannywood Hadiza gabon ta soki jarumi Ali nubu kan shishigin da sukayiwa jaruman shirin Big Brother.

A ranar Lahdin data wuce aka sami damar kammala shirin Big brother naija kashi na 6 wanda kamin a kammala shirun sai da aka shafe tsawan watanni 3 ana yin aikin shirin wanda ake haska shi a gidan Talabijin din StarTime, inda aka sami wani inyamuri mai suna Whitemoney inda ya sami rasarar lashe gasar da akayi sannan ya sami zunzurutun makudan kudade har Naira Miliyan 90.

Wannan shirin da akayi na Big brother ya sami kalubale daga wajan malaman addinin musulinci da kuma na kiristoci duba da yadda aka gudanar da al’amuran da sukaci karo da koyarwar addinai 2, amma sai dai kuma matasa da manya wanda suke da yawan shekaru sun maida hankalun su wajan kallon shirin da kuma bibiyar sa duk da tabargazar da ake a ciki.

Bayan wasu lokuta da kammala wannan shirin na Big brother zakaran da ya lashe gasar mai suna Whitemoney da kuma wanda yake biye masa har ma da wadanda suke cikin shirin sun tsabiri Kano, domin wani shagalin bikin taya murna na kamfanin Multichoice masu DS Tv da kuma GoTv wanda suka shirya, inda aka gudanar da shagalin bikin a dakin taro na tashir Guest Palace dake jigar Kano.

Inda jaruman masana’antar kannywood suka halarci wajan wannan shagalin bikin tare dayin hotuna da bidiyoyi na taya inyamurin da ya lashe wannan gasar mai suna Whitemoney, cikin jaruman kannywood wanda suka halarci wajan wannan taron shagalin bikin sun hada da, Jarumi Ali nuhu, Jarumi Adam a zango, Jarumi Almustapha, Abubakar bashir mai shadda, Baba karami, Ibrashim mindawari.

Domin kuji cikekken labari kan sukar da jaruma Hadiza gabon tayiwa Ali nuhu sabida halartar wajan wannan shagalin na Big brother sai ku kalli bidiyon dake kasa.

Ga bidiyon nan sai ku kalla sannan kuma muna bukata ku danna alamar subscribe domin samin labaranmu a duk sanda muka wallafa.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button