Fitacciyar jarumar Nollywood Mo Bimpe ta Musulunta bayan ta auri Musulmi ta canja sunanta zuwa Rahmatullah.

Fitacciyar jarumar Nollywood Mo Bimpe ta Musulunta bayan ta auri Musulmi ta canja sunanta zuwa Rahmatullah.

Wani rubutu da jarumi Adedimeji Lateef ya wallafa a shafin shi na kyakkyawar amaryar shi Mo Bimpe ya nuna cewa tuni jarumar ta canja sunanta zuwa na Musulmai.

A baya dai jarumar tana bin addinin Kiristanci sau da kafa amma sakamakon auren jarumin da tayi wanda yake shi Musulmi ne ya sanya ta canja addini zuwa addinin Musulunci.

A rubutun da Adedimeji ya wallafa wanda ya yi alkawarin soyayyar shi gareta ya bayyana cewa yanzu sunanta ya tashi daga Mo Bimpe ya koma Rahmatullah.

Jaruminya ce:

Alhamdulillah Nagode wa Allah Adebimpe Rahmatullah ina so ki sani cewa ina sonki kuma zan kasance a tare dake a koda yaushe Ina miki barka da zuwa duniya ta.

Masoyan su sunyi ta sanya musu albarka tare da fatan alkhairi a gare su kan wannan sabuwar rayuwa da za su fara a tare.

Kwanaki kadan bayan anyi bikin gargajiya a jihar Ekiti Adedimeji Lateef da Mo Bimpe an daura musu aure kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a ranar Laraba 22 ga watan Disambar shekarar 2021.
A wani bidiyo da aka nuno ma auratan a shafukan sadarwa an nuno Adedimeji da Rahmatullah cikin fararen kaya sun rike juna cikin shauki na soyayya.

Bayan haka kuma an dauki jaruman hotuna da dama na aure a cikin dakin hotel da suka kama a lokacin bikin na su.

Haka kuma idan ba a manta ba a makon da ya gabata mun kawo muku labarin yadda fitacciyar jarumar Bollywood Sanam Chaudhry ta yi sallama da harkar fim.

To jama’a zamuso mukarɓi ra’ayoyin akan aukuwar wannan don jin tabakinku zamuso kubiyomu kaitsaye tasahinmu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button