Abin day faru da jaruma Maryan booth wanda aka bayyana hoton tsiraicinta yana neman faruwa ga wata mawakiya

Abin day faru da jaruma Maryan booth wanda aka bayyana hoton tsiraicinta yana neman faruwa ga wata mawakiya

Abin daya faru da jarumar masana’antar kannywood Maryam booth a kwankin baya wanda aka bayyana hotunan tsiraicinta a kafafan sada zumunta, yana shirin faruwa da wata mawakiyar turanci da yarbanci Tiwa savage.

Ficacciyar mawakiyar turanci da yarbanci Tiwa savage ta bayyana cewa wani mutumi yana yi mata barazana da cewa, zai bayyana wasu hotunanta da bidiyo wanda saurayinta ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

A lokacin da Tiwa savage take tattaunawa da wata tashar Radio a kasar Amurka, Tiwa savage ta fadi cewa bazata biya ko asi ga wanda yake mata barazanar zai bayyana hotuna da bidiyon nata ba.

Da farko dai mutumin ya fara tura sakon barazanar ne ga wani manajan Tiwa savage a ranar Laraba, sannan kuma nan take mutumin ya sanar da ita adadin kudin da yake bukata ko ya wallafa bdidyon, BBC Hausadailytime ita ta wallafa labarin.

Mawakiya Tiwa savage ta shaida cewa: Saurayinta ne bisa kuskure ya wallafa hoton nata a shafin sa na sada zumunta amma nan take ya goge hotunan, sai dai tuni mutumin da yake mata barazanar yayi saurin sauke hotunan da bidiyon.

Sannan kuma Tiwa savage ta bayyana cewa: a yanzu haka saurayin nata yana cikin halin damuwa kan wannan lamarin.

Tiwa savage ta kara da cewa: Da farko bataji dadin faruwar wannan lamarin ba, amma bazata amince ayi amfani da wannan damar wajan bata mata suna da durkusar da ita ba.

Wannan ita ce mawakiya Tiwa savage.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button