Mai Tsananin Rabo Ne Kawai Zai Iya Ganin Karshen Mulkin Buhari A Raye – PDP

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta ce mai tsananin rabo ne kawai zai iya ganin karshen mulkin Buhari a raye saboda tsananin kuncin da talakawa ke ciki.

PDP ta bayyana hakan ne a cikin sakonta ga ’yan Najeriya na sabuwar shekarar 2022.

A cikin sanarwar da Sakataren Yada Labaranta, Debo Ologunagba, ya fitar ranar Juma’a, PDP ta taya ’yan Najeriya murnar shekarar.

Jam’iyyar, ta kuma roke su da su farfado da kyawawan halayen soyayya, hadin kai da mutunta juna, a kokarin da ake na samun shugabanci nagari.

A cewar PDP, ba karamin abin mamaki ba ne yadda kasar nan ta tsallake yadda ake ci gaba da take hakkin dan Adam da kashe-kashe da tabarbarewar tattalin arziki da yadda ayyukan raya kasa suka tsaya cak, duk a saboda rashin iya mulkin gwamnatin APC.

Sai dai PDP ta ce sabuwar shekarar wata dama ce ga ’yan Najeriya don su ajiye dukkan banbance-banbancensu wajen tunkarar tarin kalubalen da kuma ceto kasar daga halin ni-’yasun da ta fada.

Ta kuma ce kamata ya yi gwamnatin ta APC ta yi amfani da sabuwar shekarar wajen sake duba manufofinta a Najeriya saboda takalawa na cikin tsananin kunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button