Gwanatin Tarayya Zata Ƙara Buƌe N-Power Programme

Kamar yadda mutanen wannan kasa tamu mai albarka suka shaida game da tsarin ƌaukar ma’aikata na wani lokaci domin ƙakile zaman kasha wando da domin karawa matasa ƙaimi domin su dogara da kansu duba yadda ake ƙara yawa na marar sa aikin yi a duk shekara lallai hakan zai taimaka matuƙa.

Shirin N-Power Programme ya fara daukar ma’aikata tun farkon Gwamnatin ta shugaba Muhammadu Buhari daga bangarori da dama kama daga aikin lafiya, noma, da kuma koyarwa, tun a fari dai an dauki ma’aikata wato wadanda akeyiwa laƙabi da batch A, sannan B da kuma C wanda sune ludayinsu ke kan dawo a halin yanzu

Kamar yadda muka anbata a sama cewa za’a sake daukar  sababbi wanda zazu zama batch D Kenan a nan gaba kaƌan wanda mun sami wannan labarine daga majiyamai ƙarfi.

Munyi wannan rubutu ne domin ya isa izuwa miliyoyin mutane domin su zama cikin shiri wanda da zarar an buƌe portal zamu sake rubutu akai domin ƙara sanarwa.

Abinda ake buƙata domin yin rijista:

Duk wanda yake da sha’awar yin rjistar N-Power ba tare da wata matsala ba to tabbas yana buƙatar yasan waƌan nan abubuwa domin da yawan mutane sunyi rijista a wannan sabon ƌdaukar da aka yi amma kuma sunan su bai fito ba cikin jerin waƌanda suka samu nasara kuma hakan ya faru ne sakamakon rashin bin ƙa’ida wajen yin rijistar.

  1. Wajibine wanda zaiyi wannan rijista ta N-Power yazama ƌan Najeriya.
  2. Haka na wajibine yazama yana da BVN da kuma Lamabar Account ma’ana yazama ya buƌe account na Banki.
  3. Yazama ya Mallakii Katin shaidar zama ƌan ƙasa ko kuma raogowar katin shaidar da Gwamnati ta yarda dashi.
  4. Sai ya kasance sunan sa yayi daidai da na kan katin shaidar da zaiyi amfani da shi kuma yazama dai-dai da bayanan banki, ma’ana babu wani ban-banci.
  5. Bugu da ƙari kada asami ban-banci suna tsakanin takardun makaranta, banki, katin shaida.

Da zarar komai ya kammala kamar yadda aka lasafta, ana buƌewa sai a garzaya izuwa café mafi kusa domin yin rijistar akan lokaci ko kuma kayi amfani da wayar hannu domin yin rijistar kana daga ƌakinka.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button