Fyade Da Luwadi Ne Kan Gaba Cikin Laifukan Da Aka Fi Aikatawa A Jigawa A 2021 – Rahoto

Wani rahoto da Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta fitar, ya nuna cewa fyade da luwadi ne ke kan gaba a cikin manyan laifukan da aka fi aikatawa a Jihar a shekarar 2021.

Alkaluman na zuwa ne duk kuwa da tsauraran dokoki har guda biyu da Jihar ta kirkiro don yaki da matsalar.

A cewar rahoton dai, daga cikin manyan laifuka 196 da aka samu rahoton aikata su a Jihar a cikin shekarar tsakanin watan Janairu zuwa Disamba, fyade ne ke kan gaba har kusan sau 90, sai luwadi mai biye masa baya da aka samu rahotonsa sau 31.

Sauran laifukan da ke kan ga sun hada da rikicin ma’aurata da aka samu sau 27, fashi da makami sau 20, garkuwa da mutane sau 18, damfara da hatsari sau uku-uku da sauransu.

A ranar 21 ga watan Fabrairun 2021 ne Gwamnan Jihar, Muhammad Badaru Abubakar ya sanya hannu a kan dokar da ta hana cin zarafin dan Adam ta VAPP, wacce Majalisar ta amince da ita.

Dokar dai ta tanadi hukuncin daurin rai da rai ga duk wanda aka samu da laifin aikata fyade ga yara ’yan kasa da shekara 14.

Da yake tsokaci a kan rahoton, Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Jihar, Dokta Musa Adamu Aliyu, ya ce an samu ci gaba sosai a shekarar wajen gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.

Ko da yake ya ce ya zuwa yanzu ba a kai ga yanke hukunci ba a karkashin sabbin dokokin, amma ya ce yana da kwarin gwiwar za a samu nasarar yin hakan, la’akari da jajircewar ma’aikatarsa.

Kwamishinan ya ce an kuma gurfanar da mutum 84 a gaban Manyan Kotunan Jihar da ke hedkwatar masarautun Jihar guda biyar da ke Dutse da Hadejia da Gumel da Kazaure kuma Ringim.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button