Ba ma son ‘yar mu ta sha wahala: Iyayen amarya sun fasa aurawa ango ‘yarsu bayan ganin gidan da za ta zauna

Wata budurwa ‘yar Najeriya mai suna Maryam Shetty a Facebook ta yada wani labari a shafinta, inda ta zayyana yadda aka fasa wani aure bayan samun karamar matsala.

Kafin ta ba da labarin, budurwar ta rubuta cewa al’adar nuna fifiko ya zama ruwan dare a yankin Arewacin kasar nan kuma iyaye ne ke aiwatar da shi.

‘Yar mu ba za ta zauna a nan ba

Ta bayyana cewa kafin a soke auren, iyayen amaryar sun ji cewa gidan angon sam bai musu ba, kuma bai dace da matsayin ’yar su ba.

Ango da danginsa sun tubure kan bukatar gidansu amarya

Don gyara lamarin zuwa yadda suke so, dangin amarya sun ba su wani sabon gida ga ma’auratan; tayin da ango ya ki amincewa dashi tare da danginsa.

Maryam ta ce mutumin dai ba talaka bane domin shi mutum ne mai tarin ilimi kuma yana da aiki mai tsoka.

Ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, rubutun ya tattara fiye da sharhi 400 tare da dubban dangwale bayan da aka sake yada shi ta shafin Instagram na @instablog9ja.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

fashiondoctor19 ya ce:

“OMO a rayuwar nan, kawai ka nemi kudi don kada a raina ka. Orichirichi.”

foodie_mai_cooks ya ce:

“Na yarda da labarinta fah. Mutanen Arewa ba sa wasa! Amma wasu na ganin cewa ‘yan matan Owerri/Igbo ne suka fi kowa tsadar aure da bukatun aure. Una never see chunchin.”

beighdiva50 ya ce:

“Matsa ta isa kowane bangare na Najeriya.”

officialpeaceessien94 ya ce:

“Bani da ta cewa… Mutumin tsallake rijiya ta baya.”

symplychi_oma ya ce:

“Kuma waccar dukiyar da kudin gwamnati ake sacewa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button