Film 10 Na Kannywood da Suka Shahara a 2021

Babu shakka, abubuwa da dama sun faru ga Kannywood da mambobinta a wannan shekarar ta 2021. Wadannan kuwa sun hada da na farin ciki da akasin haka.

Manya daga ciki su ne; mutuwar tsohuwar tauraruwa Zainab Booth, da ta tauraron wasan barkwanci kuma ƙwararren mai ɗaukar hoto, Ahmad Aliyu Tage da kuma ta Sani Garba SK.

Sannan ga matsanancin ciwo da ya addabi tauraruwa Maryam Yahaya. Ga kuma rikice-rikice da suka ɓarke tsakanin Adam A. Zango da wadda yake reno a harkar fim, Ummi Rahab. Da rikicin Umma Shehu da hukumar Hisba ta Kano, da kuma tsakanin wasu daraktoci da shugaban hukumar tace fina-finai, Malam Isma’il Na’abba Afakallahu.

A ɗaya ɓangaren kuma, abubuwan farin ciki da dama su ma sun faru ga ‘yan Kannywood. Sun samu ƙarin sinima mai nuna fina-finansu a Kano; sannan babbar manhajar kallo ta intanet wato (NetflixNaija) ita ma ta tuntuɓe su. Ga taurari irin su Zahra Diamond da Maryam Waziri da kuma Garzali Miko sun yi aure a 2021.

Duk da cewa fina-finai masu dogon zango sun kusan mamaye na al’ada da ake nunawa a sinima, waɗannan su ne suka fi shahara a cikin fina-finan Kannywood da suka fita a wannan shekara.

1.Ka Yi Na Yi

Shi wannan fim ya zama zakara cikin duka fina-finan Kannywood ba kawai na iya wannan shekarar ba, don kuwa, shi ne na farko da aka taba samun kuɗi sama da Naira miliyan biyar yayin nuna shi a sinima. Amma hakan ba yana nufin ya fi sauran kyau ko ma’ana ba ne.

Duk da dai masu fim ɗin sun ce ci gaban Kalan Dangi ne, labarin ba ɗorawa ya yi daga inda wancan ya tsaya ba, sannan wasu taurarin da suke cikin wannan, babu su a wancan.

Sai dai kamar Kalan Dangi, shi ma Ka yi Na Yi an shirya shi ne da salon barkwanci kuma jigonsa ya dace da halin da muke ciki.

Fim ne game da yadda ‘yan damfara suke cin karensu ba babbaka a kafofin intanet da harkar canjin kudade da sayar da filaye da kuma ‘yan ka-yi na-yi da suka yi katutu a kasuwanninmu.

Ba iya faɗakarwa ya yi ba, fim ɗin ya nishaɗantar sosai. Duka wadanda ke ciki sun yi ƙoƙari wajen burge ‘yan kallo musamman Sani Danja da Sadiq Sani Sadiq.

Mun jinjina wa daraktan fim ɗin, Ali Gumzak, tare da wanda ya shirya shi, Abubakar Bashir Maishadda.

2. Sarki Goma Zamani Goma

Sanannen kamfanin shirya fina-finai na Maishadda wanda haɗakarsa da darakta Ali Nuhu ta haifar da manyan fina-finai irin su Mariya (2018) da Hafeez (2019), shi ne ya sake haɗa kai da daraktan suka yi Sarki Goma Zamani Goma.

Fim ɗin ya bayar da labari ne na wasu ‘yan mata da suke yin rayuwar ƙarya da kuɗin da suke samu ta hanyar mu’amala da maza masu hannu-da-shuni.

Mahaifin ɗaya daga cikinsu, Ali Nuhu, talaka ne sosai amma ba ya karɓar komai daga hannunta, kuma kullum ƙalubalantar hanyar samun kuɗin nata yake. Su kuwa iyayen sauran ba su damu da bincikar ‘ya’yan nasu ba.

Daga ƙarshe dai dukkansu sun koyi darasi kuma suka yi nadama.

Fim ɗin ya haɗu sosai, kuma maudu’insa ya dace da wannan zamanin. Ya tattaro taurari da dama kuma dukkansu sun taka rawar gani. A cikinsu har da Aisha Najamu (Izzar So) da Rayya (Kwana Casa’in) da Minal Ahmad (Nana Izzar So), waɗanda taurari ne a fina-finai masu dogon zango. Sannan kayan da taurarin suka saka da gidajen da aka yi amfani da su suma suna da jan hankali.

3.Zainabu Abu

Wannan kuma fim ne na soyayya wanda ya shafi sadaukarwa. Ya bayar da labarin wani saurayi ne mai suna Habeeb (Umar M. Sharif) da ya yarje wa masoyiyarsa Zainabu (Mommy Gombe) ta auri yayansa Auwal (Ali Nuhu).

Auwal ɗin yana da ciwon zuciya kuma likita ya tabbatar ba zai rayu sama da wata shida ba. Don haka, Habeeb ya sadaukar da Zainab ne da nufin za ta dawo gareshi idan Auwal ya rasu.

Amma abin mamaki sai Auwal ya warke kuma ya ci gaba da rayuwa bayan wata shidan.

Daga nan sai rikici ya ɓarke bayan da Habeeb ya nemi a kashe auren amma aka ƙi.

Fim ɗin ya ƙayatar yadda ya kamata. Yana da waƙoƙi masu daɗi kuma an saka su a guraren da suka dace. Sannan ‘yan wasan ciki, wadanda aka ambaci sunayensu a sama, sun yi ƙoƙari sosai.

Ali Nuhu ne ya bayar da umarni yayin da Bashir Maishadda ya shirya.

4.Tsakaninmu

Fahad (Umar M. Sharif) ɗa ne ga wani hamshaƙin ɗan kasuwa Alhaji Rabi’u (Nura Hussaini), kuma yana matuƙar ƙaunar wata ‘yar talaka mai suna Nafisa (Maryam Yahaya). Amma tilas ya hakura da ita ya auri Rumaisa (Maryam Booth) ɗiya ga Farfesa Tahir (Ali Nuhu), wato abokin mahaifinsa, domin ya cika burin mahaifin nasa.

Bayan auren kuma, sai zaman ya ƙi daɗi kasancewar ita Rumaisan a ƙasar waje ta yi karatu kuma ta ɗauko ɗabi’un Turawa, don haka ta kasa sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na aure.

Bayan da abin ya ci tura dai, sai Fahad ya sake ta. Wannan ne ya kawo ƙarshen abotar iyayensu ta tsawon shekara 40.

Daga baya kuma Fahad ya sake koma wa masoyiyarsa ta asali, Nafisa, suka farfaɗo da soyayyarsu kuma suka yi aure a ƙarshe.

Fim ɗin ya sha yabo daga masu kallo saboda yadda ya ilimantar kuma ya nishaɗantar a lokaci guda.

Kowanne tauraro ya yi ƙoƙari wajen taka rawar da aka ba shi. Mai ba da umarni wato Ali Nuhu, da mashiryinsa, Abubakar Bashir Maishadda, sun cancanci a jinjina musu.

An ɗauki fim ɗin da kyau, hotunan sun fita tarwai. Idan ka kalle shi zai ja hankalinka.

5.Fanan

Labari ne na wani mai suna Kamilu (Yakubu Muhammad) wanda yake zaune lafiya da matarsa Fanan (Sabeera), amma sai ya fara yi mata wulaƙanci rana tsaka. Daga ƙarshe ma ya sake ta sakamakon haɗuwa da ya yi da wata mata mai kuɗi, Madam Jessica (Rahama M.K).

Jessica ta yi masa alƙawarin za ta aure shi kuma ta taimaka a yi masa babban muƙami a wani kamfani. Daga bisani kuma sai ta watsar da shi ba tare da ta cika alƙawuranta ba.

Daga nan sai Kamilu ya fara ƙoƙarin dawo da aurensa da Fanan. Sai dai loƙaci ya riga ya ƙure masa domin Fanan tuni ta auri wani hamshaƙin mai kuɗi, Alhaji Sammani (Sani Danja).

Ba shakka wannan shirin ya sami karɓuwa sosai saboda ficen da waƙarsa ta yi tun kafin fitarsa, da kuma yadda furodusansa, Mansura Isah, da sauran abokan aikinta suka yi ruwa da tsaki wajen ganin ya karaɗe ko’ina.

6. Bana Bakwai

Shi wannan fim, wanda na kamfanin FKD ne, yana ɗaya daga cikin fina-finan Kannywood da suka fi dacewa da yanayin da muke a yanzu. Ya yi nuni ne ga yadda rashin aikin yi da wofintar da ‘ya’ya ba kulawa da kuma yadda sake-saken aure kan jawo ta’addanci da rashin tsaro.

Wannan fim ya cancanci yabo saboda ma’anar jigonsa da kuma yadda aka yi amfani da kayan aiki masu inganci, da ƙwarewa wajen yinsa.

Duk da cewa an fara nuna shi tun a ƙarshen shekarar 2020, an ci gaba da nuna shi har cikin wannan shekarar ta 2021. Hakan ne ya ba shi damar shigowa cikin wannan jerin.

Bugu da kari, kowanne daga cikin taurarinsa sun yi matuƙar abin da ya kamata. Mun jinjina musu da su da daraktan Ali Nuhu, da furodusa Nazifi Asnanic.

7. Makota

Wannan kuma fim ne na barkwanci da yake ɗauke da taurari da dama. Fim ne a kan irin takun-saƙar da ake samu tsakanin makota.

Ali Nuhu da Musa Maisana’a makota ne a kasuwa kuma ba sa ga miciji. Haka ita ma Aina’u Ade, wadda ta fito a matsayin Bayarabiya, kullum rikici take da makocinta, Rabi’u Rikadawa, da iyalinsa.

Suma iyalin Rikadawan zaman doya da manja suke. Matarsa ta farko, Ladidi Fagge, ‘yarta, Amal Umar kamilalliya ce, amma Maryam Yahaya, ‘yar matarsa ta biyu, Saratu Daso, ba ta da kamewa. Shi kuwa ba ya tsawatar wa Maryam ɗin saboda talaka ne kuma samarinta suna ba shi abin hannu.

Haka dai aka yi ta rikici, a ƙarshe kuma komai ya warware.

Fim ɗin ya nishaɗantar sannan kuma ya faɗakar kwarai da gaske kuma taurarin ciki sun yi ƙoƙari sosai.

Mandi Birget ne ya shirya shi, Ali Gumzak kuma ya bayar da umarni.

8. Avenger

Avenger, wanda fim ne na kamfanin MM Haruna, an shirya shi ne da salon faɗa kuma aka gabatar da shi a cikin harshen Ingilishi.

An gina labarin fim ɗin a kan Jamal, wanda tun yana ƙarami aka kashe iyayensa kuma ya taso da wutar fansa a zuciyarsa.

Bayan da ya fara farautar waɗanda mariƙinsa Sani Mu’azu ya faɗa masa cewa su ne suka kashe iyayen nasa ne kuma sai ya gano ashe ba haka ba ne.

Sani Mu’azun shi ne haƙiƙanin wanda ya jagoranci kisan iyayen nasa, kuma a yanzu yake amfani da shi.

Ai kuwa sai Jamal ya sha alwashin ɗaukar fansa a kansa. Shi kuma ya ɗauko hayar tawagar su Shu’aibu Kumurci don su kare shi. Haka dai aka yi ta gumurzu da Jamal har zuwa ƙarshe.

Ko da yake akwai alamun fim ɗin kwaikwayoshi aka yi daga wani waje, an yi ƙoƙari sosai wajen gabatar da shi.

Fim ɗin ya yi fice sosai, kuma yana cikin fina-finai mafiya shahara na wannan shekara. Nazifi Asnanic da Usman Mu’azu ne suka shirya shi, Bature Zambuk kuma ya bayar da umarni.

9. Gari Guda

Yayin da ake ta ƙalubalantar Kannywood a kan irin fina-finan da suke yi, kamfanin ‘Islamic Film Empire’ ya zo da wannan shirin da ya bambanta da sauran mai suna Gari Guda.

Gari Guda wani fim ne da ya nuna yadda ‘yan ta’adda suke addabar ƙauyukan arewacin Najeriya, suke sace mutane domin kuɗin fansa.

Fim ɗin ya matuƙar nuna abubuwan da suke faruwa a zahiri. Ya nuna ainihin yadda yankin arewacin Najeriya yake, ya kuma nuna irin yadda ‘yan ta’adda suke zuwa ƙauyuka a babura su yi ɓarin wuta su sace mutane, kamar a gaske.

Duk da cewa mashiryan shirin da ma ‘yan fim din duka ba sanannu ba ne, sun cancanci a yaba musu, don yin irin wannan fim ɗin ba ƙaramar jarumta ba ce.

Sai dai a ƙoƙarinsa na dacewa da addini, an ɗan samu ƙarancin nishadantarwa a cikin fim ɗin. Amma ya ilimantar kwarai da gaske.

Safiyan Lawan Kabo ne ya shirya kuma ya bayar da umarni.

10. Juwairiyya

Shi kuma wannan labari ne na soyayya tsakanin Nura (Garzali Miko) da Juwairiyya. Suna son junansu sosai, amma haka yayanta ya aura mata Adam A. Zango saboda shi Nuran ba shi da sana’a.

Bayan auren kuma sai ta kasa sakin jikinta da mijin (Adam A. Zango) saboda matsanancin son da take wa Nura.

Yayin da mijin ya fahimci haka, sai ya sake ta, kuma ya yi alƙawarin ba wa Nuran aiki saboda ya iya aurarta. Amma da ta dawo gida, sai ta samu Nuran ya faɗa shaye-shaye saboda rasa ta da ya yi. Ita kuwa sai ta ƙi aurarshi, ta koma gidan tsohon mijinta.

Duk da fim ɗin na soyayya ne, amma yana ɗauke da darussa. Taurarin cikinsa duka sun yi kokari, musamman ma Garzali Miko.

Hafizu Bello ne ya bayar da umarni yayin da Alhaji Sheshe kuma ya shirya shi.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button