Buhari Ya Ceto Najeriya Daga Durkushewa A 2015 – Malami

Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnati, Abubakar Malami SAN, ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ceto Najeriya daga durkushewa cikin shekararsa ta farko bayan karbar mulki a 2015

Malami ya ce Buhari ya ceto Najeriya yayin da take shirin rushewa sakamakon karyewar tattalin arziki da sauran matsaloli cikin kankanin lokaci.

Ministan ya bayyana hakan ne cikin wani shiri a Gidan Rediyon Kano ranar Lahadi, inda ya ce tattalin arzikin ya samu mummunan koma baya kafin zuwan Buhari.

Ya ce abin da Buhari ya cimma cikin kankanin lokaci ko kasashen da suka ci gaba ba za su iya ba.

“Shugaban Kasa ya cimma wannan nasara a cikin kasa da shekara daya, ya ceto tattalin arzikinmu daga durkusewa. Ba kowane shugaba ne zai iya yin abin da ya yi ba. Ko kasashen da suka ci gaba sun fuskanci yanayi irin wannan kafin su farfado.”

Kazalika, Malami ya ce Shugaba Buhari bai tsaya nan ba, ya kirkiro shirin N-Power da tallafin COVID-19, don cire miliyoyin ’yan Najeriya daga kangin talauci.

Game da bangaren tsaro kuwa, Ministan ya ce Buhari ya ceto yankin Arewa maso Gabas, daga ta’addancin Boko Haram.

“Kafin zuwan Buhari, akwai matsalolin tsaro da yawa, musamman a Arewa maso Gabas, amma a yanzu mun yi nasarar dakile hare-hare. Yanzu a kan shafe tsawon lokaci kafin ka ji an kai hari kasuwa, wuraren ibada da sauransu,” cewar Malami.

Har wa yau, ya bayyana yadda Gwamnatin Tarayya da jami’an tsaro ke aiki tukuru wajen ganin an kawo karshen ayyukan ’yan bindiga a Arewa maso Yammacin kasar nan.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button