Trending

Fadar Shugaban Kasa:Garba Shehu,Dogarin Shugaban Kasa, Babban Mai Tsaron Shugaban Kasa Sun Kamu Da Korona.

Fadar Shugaban Kasa:Garba Shehu,Dogarin Shugaban Kasa, Babban Mai Tsaron Shugaban Kasa Su Kamu Da Korona.

Fadar Shugaban kasar nigeria dake Aso Rock Abuja, ta bada labarin cewa wasu daga cikin hadiman Shugaban kasar su kamu da Korona.

Gidan jaridar Premium times ta bayyana cewa hadiman Shugaban kasar da suka kamu sune makusantar shugaban kasar.

Wadan da suka kamu da jiyar sune, Dogarin Shugaban kasar, Yusuf Adado, da Babban mai Bawa Shugaban Kasar tsaro, Aliyu Musa da kuma kakakin shugaban Garba Shuhu,da kuma ministan yada labarai da al’adu Lai Muhammad.

Fadar Shugaban kasar tace an gwada su kuma an tabbatar da su samu kamuwa da cutar cikin wannan satin.

Sai dai Fadar ta bayyana manema labarai cewa duk wadan da suka kamu da jinyar basu shiga yanayin da zasu gala baita ba,domin su samu Riga kafin korona.

Bayan tabbatar da hakan Garba Shehu ya bayyana cewa bashi da tabbacin Akan abin da suke fadi, game da kamuwar sai dai daga baya yace, ya kamu Amma ba mai tsanani ba.

Sanan Garba Shuhu ya Kara da cewa jinyar Bata hanashu komai ba domin yanzu ma ya gama motsa jiki da yake yi na tsawon awa daya.

Bayan da haka a wannan satin ne dai shugaban kasar ya karbi zagayen allurar cutar Karo na uku.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button