Buhari: Alkawarin da Buhari ya Dauka wa Yan Nigeria, kafin Watan sa Sha Bakwai Akan mulki ya kare.

Buhari: Alkawarin da Buhari ya Dauka wa Yan Nigeria, kafin Watan sa Sha Bakwai Akan mulki.

Shugaba Muhammad Buhari a jiya alhamis da yayi dede da 23/12/2021,yayi bayani cewa gwamnatin sa zata Kara zage damtse wajan ciyar da nigeria gaba.

Yayin bayanin nasa ne yace nan da wata goma Sha Bakwai zai sauka Kan Mulkin kasar a watan may, 2023, Zai bayar da Mulkin kamar yadda kundin tsarin Mulkin kasar ya tanada.

Shugaban yayi bayanin nasa ne a in da yake Bude sabon aiki a maiduguri da Wanda aka yiwa aikin da Oriental Energies Resource Ltd Hanger da attajirin nan Alhaji Muhammadu Indimi.

Shugaban kasar ya kaddamar da ginin Tijjani Bolori memorial secondary School da kuma Babbar gadar Sama ta farko a maiduguri.

Shugaban ya Kara da cewa nayi rantsuwa zan bi kundin tsarin kasa, don haka zan bar mulki nan da wata goma Sha Bakwai. Sannan Ina mai addu’ar duk Wanda zai gajemu zai bi hanyar da zai kawo karshen tabbarewar tsaro da kuma bun kasa kasa.

Nigeria zata ci gaba ne idan matsalar tsaro da habbaka tattalin arzikin kasa da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button