Gwamnatin Kaduna Ta Fitar Da Sunayen Mutanen Da ’Yan Bindiga Suka Kashe A Giwa

Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana sunayen mutane 29 daga cikin 38 din da ’yan bindiga suka kashe a Karamar Hukumar Giwa da ke Jihar a karshen makon da ya gabata.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar da Kwamishinan Tsaro da Al’amura Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ya fitar ranar Lahadi.
Kimanin mutune 38 ne ‘yan bindiga suka bi har gida suka kashe a kauyukan Kauran Fawa, Marke da Ruhiya da ke gundumar Idasu a Karamar Hukumar Giwa a ranar Asabar din ta gabata.
Gwamnatin ta ce ta gano sunayen mutane 29 daga cikin wadanda abin ya shafa, yayin da sauran taran ba a san ko su waye ba, har zuwa lokacin da aka fitar da sanarwar.
Ga jerin sunayen 29 da aka tabbatar kamar haka:
- Rabi’u Wada
- Salisu Boka
- Alh Nura Nuhu
- Alh Bashari Sabiu
- Alh Lawal Dahiru
- Abbas Saidu
- Inusa Kano
- Malam Lawal Nagargari
- Malam Aminu
- Lawal Maigyad
- Alh Mustapha
- Lawal Aliyu
- Sale Makeri
- Sani Lawal
- Auwal Umar
- Jamilu Hassan
- Badamasi Mukhtar
- Malam Jibril
- Lawal Tsawa
- Sule Hamisu
- Sadi Bala
- Kabiru Gesha
- Abubakar Sanusi
- Saiph Alh Abdu
- Haruna Musa
- Lawal Hudu
- Malam Shuaibu Habibu
- Malam Yahaya Habibu
- Abubakar Yusuf
Cikin mako guda ’yan bindigar sun kashe mutane da dama a yankunan Kananan Hukumomin Zangon Kataf, Chikun, Birnin Gwari, Igabi da kuma Kauru duk a Jihar ta Kaduna.