Kano: Ya Kasa Gane Gidan Su A Jihar Kano Bayan Shafe Shekaru A Makaranta

Daga: Fahad Kabir Maitata

Wani matashi mai suna Abdulkarim Garba wanda dan asalin jihar Kano ne, yayi batan kai inda ya nemi gidan su ya rasa bayan ya dawo daka makarantar Allo.

Matashin wanda akakai shi karatu a makarantar Allo a garin Maigatari ta jihar Jigawa wajan malam Musa.

Ya kuma shafe akalla shekaru Takwas acan, yanzu ne kuma da ya dawo Kano ya kasa gane unguwar su dama gidan su ina yake.

Sai dai hukumar Hisbah a jihar ta karbe shi, inda ta dukufa wajan lalubo inda ya ke domin mikashi ga yan uwan sa.

Mai magana da yawun hukumar Lawan Ibrahim Fagge a ranar Juma’a ya tabbatar wa da jaridar AlkIblah cewa yaron yana hannun su.

Ya kara da cewa, matashin ya ce abaya dai yasan akwai gidan yan uwan su a Fanisau kusa da gidan sarki, kuma sunan su shine.

Aisha da Amina kuma sunan mahaifiyar su Sa’adatu.


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button