Babu ɗan ta’addan da zai shigo jihata ya fita da rayuwarsa, Gwamnan Arewa

Kogi – Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sha alwashin ɗaukar tsattsauran mataki kan yaan ta’addan dake shigowa jiharsa domin neman mafaka.

Dailytrust ra ruwaito gwamnan na cewa matukar suka shigo jihar, to babu makawa zasu gamu da ajalinsu.

Gwamna Bello ya yi wannan furucin ne yayin da ya karɓi bakuncin shugaban ƙaramar hukumar Yagba West, Pius Kolawole, domin tattaunawa kan fashi da makami a yankinsa da kuma matakan da aka ɗauka.

Ya ƙara jaddada kudirin gwamnatinsa na haɗa kai da dukkan hukumomin tsaro wajen tsaftace jihar daga mutane masu tunanin aikata ta’addanci ba tare da tausayi ba.

Duk wani ɗan ta’adda ba zai fita da rai ba – Bello

Yahaya Bello ya bayyana cewa babu wani ɗan ta’adda, da zai shigo jihar Kogi domin aikata ta’addancinsa, kuma ya fita a raye.

Gwamnan yace:

“Idan yan ta’adda kamar 20 ne suka shigo jihar Kogi, to ko guda ɗaya ba zai fita da rayuwarsa ba.”

Gwamna Bello yace har yanzun akwai burbushin masu aikata manyan laifuka a jihar, ya gargaɗi cewa duk wanda ya shiga hannu zai fuskanci fushin doka.

Hakanan kuma ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar Yagba Wes bus ajajircewarsa da kuma kokarin da yake yi wajen shawo kan lamarin.

Wace nasara aka samu?

Tun da farko, shugaban ƙaramar hukumar, Pius Kolawole, ya shaida wa gwamnan cewa kokarin da ake cigab da yi ya fara haifar da ɗa mai ido.

Yace jami’an tsaro sun samu nasarar hallaka wasu da kuma kama wasu daga cikin yan fashin dajin da suka kai hari yankunan Egbe da Odo Ere a baya-bayan nan.

A wani labarin kuma

Source: Legit


Follow Hausadrop On Facebook

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button